24 Disamba 2020 - 13:10
Habasha Ta Harba Tauraron Dan-Adam Na Biyu

Kasar Habasha ta yi nasarar harba tauraron dan-Adam dinta na biyu, tare da taimakon kasar Sin.

ABNA24 : Da yake karin haske kan wannan batu, mataimakin babban darektan cibiyar nazarin kimiya da fasahar sararin samaniya na kasar Habasha Yishrun Alemayehu, ya bayyana cewa, tauraron dan-Adam din mai lakabin ET- Smart-RSS wanda aka harba shi a ranar Talata daga tashar harba taurarin dan-Adam dake Wenchang na kasar Sin, yana da na’urori na zamani, yana kuma iya daukar hotuna masu inganci matuka.

Ya kara da cewa, harba tauraron dan-Adam din, wani babban ci gaba ne ga kasar ta Habasha a fannoni da dama.

Yana mai cewa, cibiyar za ta ci gaba da kokarin kara karfinta a fannin kimiya da ci gaban bil-Adama.

Kasar Habashe ce dai ta zana fasalin tauraron dan-Adam din, yayin da tawagar injiniyoyin Habashan da Sin suka fito da cikakken fasali da tsare-tsarensa.

A watan Disamban shekarar 2019 ne dai, kasar Habasha ta harba tauraron dan-Adam dinta na farko, da aka yiwa lakabi da ETRSS-1 tare da taimakon gwamnatin kasar Sin.

342/